Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, Mai Girma Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Hali, ya fitar da saƙo a matsayin amsa ga wasiƙar Babban Sakataren Hizbullah da mayaƙanta.
Ga fassarar cikakken saƙon kamar haka:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
"Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku yaƙi kafiran da suke kusa da ku, kuma su ga tsanani a cikinku..."
Mai Girma Hujjatul Islam wal Muslimin Sheikh Na'im Qasim (Allah Ya ƙara masa ɗaukaka), Babban Sakataren Hizbullah na Lebanon, da kuma dukkan kwamandoji da mayaƙa masu sadaukar da kai, masu haƙuri da juriya na Hizbullah.
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.
Wasiƙarku, ya ku 'yan'uwana da 'ya'yana, ku muminai kuma jaruman mayaƙan Hizbullah masu ɗaukaka, waɗanda suka isar da saƙon juriya da tsayin daka domin ɗaukaka Kalmar Allah, da imani da alkawuran Alƙur'ani Mai Girma da manufofin Imam Khumaini da Jagoran Juyin Juya Hali Shahidi Ayatullah al-Uzma Khamenei (Allah Ya yarda da su), ta cancanci yabo da girmamawa.
A yau da al'ummomin duniya suka gaji da zalunci da ta'addancin gwamnatin Amurka da Sahyoniyawa masu aikata laifuka da rusa noma da zuriyya, babu wata hanya da ta rage face jihadi da gwagwarmaya. Tsayin daka a wannan tafarki zai ba mujahidan hanyar gaskiya nasarar da Allah Ya yi musu alkawari.
"...Kuma hakki ne a gare Mu Mu taimaki muminai."
Yanzu da Hizbullah ta Lebanon take tsaye tamkar wani katafaren dutse a gaban mummunan harin gwamnatin sahayoniyya da masu mara mata baya, wannan tsayin daka ya zama saƙo mai ƙarfafawa ga al'ummomin duniya masu son 'yanci domin kubuta daga zalunci da danniyar girman kai na duniya da 'yan amshin shatansa.
Ba tare da shakka ba, wani babban ɓangare na wannan gagarumar nasara ya samo asali ne daga haƙuri, mutunci, sadaukarwa da haɗin kan al'ummar Lebanon, musamman mutanen yankin Kudu.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ma, bisa tafarkin Jagoran Juyin Juya Hali, Shahid Imam Sayyid Ali Khamene'i (Allah Ya yarda da shi), ta ayyana kare waɗannan mujahidai mazalumai amma masu ƙarfin hali a matsayin siyasarta ta dabaru. Haka kuma ta sanya kare cikakkiyar ƙasar Lebanon da kuma kawo ƙarshen mamayar gwamnatin sahayoniyya ba tare da wani sharadi ba, a matsayin sharadi na farko na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da Amurka mai ta'addanci ta kallafa.
Tsira da rahamar Allah su tabbata ga shahidai, da waɗanda suka ji rauni, da iyalansu masu haƙuri, da muhajirai saboda Allah waɗanda suka jure wa musibu.
Amincin Allah ya tabbata ga ruhin shugaban shahidan Hizbullah, Sayyid Hasan Nasrullah, da dukkan kwamandojin farko na gwagwarmaya da sahabbansu shahidai (Allah Ya yarda da su baki ɗaya), waɗanda suka mayar da tsiron gwagwarmayar Musulunci ya zama wata bishiya mai ƙarfi, wadda asalinta yake da ƙarfi, rassanta kuma suna cikin sama. Su ne mayaƙan da da jihadi da gwagwarmayarsu suka samar wa Lebanon ɗaukaka da girma a cikin duniyar Musulunci.
A ƙarshe, ina fatan albarkacin addu'ar shugabanmu Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), nau'o'in falala da ni'imomin Allah su shafi dukkan mujahidai, shahidai, waɗanda suka ji rauni, muhajirai da iyalansu masu haƙuri.
"Kuma Mun yi nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunana a bayan ƙasa, Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada."
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.
Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i
Ra'ayinka